1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanci

Dangantakar harin jami'an Amirka da 'yan rajin Biafra

Muhammad Bello MAB
May 17, 2023

'Yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan IPOB ne sun bude wa ayarin jami'an huldar jakadancin Amirka wuta a jihar Anambra, inda mutane hudu suka halaka tare da yin awon gaba da wasu jami'ai da ake ci gaba da garkuwa da su

'Yan rajin kafa Biafra sun saba gudanar da zanga-zanga a kudancin NajeriyaHoto: Getty Images/AFP

Harin da aka kai a kauyen Atani da ke karamar hukumar Ogbaru a jihar Anambra da ke yankin na Kudu maso gabashin Najeriya na kama da kwanton bauna. Sannan maharan da ake kyautata zato 'yan rajin kafa Biafra na IPOB ne sun bude wa ayarin jami'an Amirka wuta, yayin wata ziyarar aiki a yankin. Bayanai sun tabbatar da cewa akalla mutane hudu sun halaka a harin ciki har da ma'aikatan ofishin huldar jakadanci biyu, da 'yan sanda biyu. Haka kuma 'yan binduga sun yi awon gaba da wasu mutane uku.

Hon. Abarime Christian da ke mai magana da yawun gwamnan jihar ta Anambra ya ce wannan harin ya afku ne inda babu tsaro, bai kamata jami'an su bi ba tare da sanin hukumomi ba, Iyakar jihohin Anambara da Imo na da matikar hadari, saboda nan ne sansanonin 'yan bindiga su ke.

Jagoran IPOB Nnamdi Kanu na ci gaba da zama a gidan yariHoto: DW/K. Gänsler

Alakar harin da kin sakin Nnamdi Kanu

Babu tartibin bayanai a kan dalilin wannan ziyara ta jami'an ofishin huldar jakadancin Amirka a yankin da ma yawan jami'ai da ke cikin tawagar. DW ta yi kokarin jin ta bakin Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Anambra DSP Tochukwu Ikenga, amma ya yi kememe wajen daukar waya. Sai dai wani dan jihar ta Anambra Benny Okafor da ya nuna masaniyar afkuwar wannan harin, ya ce an kashe jami'an na Amirka hudu, kuma duk 'yan Najeriya ne.

Okafor ya ce: "Ban san me ya sa gwamnati ta kasa daukar mataki ba, ko da yake kamar akwai siyasa a ciki, domin kotu ta umarci  gwamnati ta saki Nnamdi Kanu amma ta ki, kuma kin yin hakan, shi ne dalilin afkuwar ababe marasa dadin ji a yankin kudu maso gabashin Najeriya."

Antony Blinken ya taba kai ziyara a ofishin jakadancin Amirka da ke AbujaHoto: Andrew Harnik/AP Photo/picture alliance

Gwamnatin Amirka ta sanar da cewar, harin bai ritsa da 'yan asalin kasarta ba. Amma Barista Jalo, kusa a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, ya ce wannan hari na da wata manufa ta boye. 'Yan rajin Biafra na IPOB da Nnamdi Kanu ke wa jagoranci ta ayyana zaman dirshan a gida a fadin yankin na kudu maso gabashin kasar a ranar 29 ga watan Mayun 2023, wato ranar da Najeriya za ta yi bikin mika mulki ga sabuwar gwamnatin APC da Bola Ahmad Tinubu zai jagoranta.