1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tabarbarewar dangantaka tsakanin Indiya da Pakistan

Abdoulaye Mamane Amadou
February 26, 2019

Manyan kasashen duniya sun yi kira ga kasashen Pakistan da Indiya su sanya wa zukatansu ruwan sanyi, bayan wani ruwan bama-bamai da Indiya ta yi a sansanin mayakan jihadi a Pakistan

Indien Mirage 2000 Kampfjet in Unnao, Uttar Pradesh
Hoto: Reuters/P. Kumar

Manyan kasashen duniya sun soma nuna damuwa game da rikicin Pakistan da Indiya suna masu fatar kasashen biyu za su sakawa zukatansu ruwan sanyi bayan wani ruwan bama-bamai da Indiya ta yi a sansanin mayakan jihadi a kasar Pakistan.

Kasar China ta ce yaki da ta'addanci abu ne da ya shafi kasa da kasa, tana mai kiran kasashsne biyu da su zauna lafiya, a daidai lokacin da ita ma Kungiyar Tarayyar Turai, ta yi kira da kakkausar murya ga kasashen biyu, da su warware rikicin a cikin ruwan sanyi, kana EU ta ce dole ne kasashen su guji fitina.

Sai dai kiraye-kirayen kasashen duniya na zuwa ne a daidai lokacin da kasar Pakistan ta tsaya kai da fata tana mai cewa, hujjojin da Indiya ta bayar na kai mata farmakin ba su da tushe, tana alwashin daukar fansa a duk lokacin da ta ga dama.