1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Jamus da Aljeriya

Umaru AliyuJuly 16, 2008

Ziyarar shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a ƙasar Aljeriya

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: AP

Samun canjin al'amura shine abin da yake da muhimmanci a bangaren Jamus da kuma a bangaren kasar Algeria, musmaman idan aka yi batu na dangantakar ciniki, wanda shine babban abin da ya hade kasashen biyu.

Katrin Laskowski, shugaban sashen Afrika ta arewa a kungiyar hadinkai da kasashen Afrika ta Jamus tace:


Gas da man fetur sune yanzu abubuwa biyu da suka fi daukar hankali ga kowa da kowa. Algeria ita ce kasa ta ukku a jerin wadanda suka fi mallakar arzikin gas a duniya, kuma ana sane da cewar Jamus kasa ce dake da matukar bukatar gas din domin amfanin ta na yau da kullum.


To sai dai Algeria baio kamata ta maida hankaln ta gaba daya ga arzikin gas da man fetur kawai ba., ko da shike wadannan albarkatu biyu ne suke baiwa kasar kashi hamsdin cikin dari na kudaden ta gaba daya. Wajibi ne kasart ta bude kofofin ta ga wasu fannonin na tattalin arziki, idan har tana bukatar nan gaba ta sami nasarar rage matsalar rashin aikin yi a kasar. Ko da shike Algeria tana sa ran kudin da take samu daga gas da man fetur zai karu, amma wadfata da al'ummar kasar suke fatan zai samu daga man da gas, wata ci gaba rda zama mafgarki a garesu.


Sigfried Breuer, wakilin cibiyar dangantakar tattalin arziki da kasashen ketare ta Jamus a yankin Maghreb, ya baioyana ra'ayin cewar sauke tsohon Pirayim minista kasar ta Algeria da aka yi a watan Yuni, wata alama ce ta bude kofofin kasar ga wasu fannonin na tattalin arziki.


Tsohon Pirayim minista Abdelaziz Belkhadem ya kasance makusancin kungiyoyin musulmi ne masu tsattsauran ra'ayi, dake baiyana kyamar su ga tsarin tattalin arziki irin na kasashen yamma, saboda hjaka baya bada gudummuwar sa ga ci gaban tattalin arzukin kasar ta wnanan fuska., duk da sanin cewar a Algeria Pirayim minista bashi da wnai karfin iko. Shugaban kasa shine wuka, shine nama a yanke ko wane kudiri.


Abdelaziz Belkhadem ya rika mukamin Pirayim ministan Algeria tsawon shekaru biyu. A Tsakanin wnanan lokaci, an kasa samun nasarar aiwatar da shirin da aka sanar na gyara ga tsarin tattalin arziki. Yanzu kuwa aiwatar da wnanan shiri ya tattara ne a hannun Ahmed Ouyahia, wanda mai matsakaicin ra'ayi ne a fannin tattalin arziki. A game da yan kasuwa da masu masana'antun Jamus, ko da shike zasu ci gaba da takara da takwearforin su na Faransa, amma taken Made in Germany, wato darajar kayaiyakin da aka yi a Jamus yana da muhimmanci, kamar yadda Katrin Laskowski ta nunar.

Cibiyar dangantakar ciniki da kasashen ketare ta Jamus tace yanzu haka kamfanonin kasar kimanin dari da hamsin ne suke aiyukan su a Algeria. Jamusawa ne suke aikin gina hanyoyin jirage na karkashin kasa a Algiers, uma Jamusawan ne suka karbi masana'antun yin sabulun wanki a kasar ta Algeria, kuma sune aka basu aikin gina daya dagha ciin masallatan da suka fi girma a duniya a can.


Katrin Laskowski tace kamfanoni da masana'antun na Jamus, da alamun babu abin da ya dame su da gaskiyar cewar ana keta hakkin yan Adam a kasar ta Algeria. Abin dake da muhimmanci shine, Jamusawan wajibi ne su nemi wata kafa ta samun gas, a kokarin su na rage dogaro da Rashqa. Algeria kuwa tana iya cika burin na Jamus game da haka.