Dangantakar Jamus da Tunusiya
March 3, 2017Shugabar gwamnatin Jamus din Angela Merkel ce ta bayana hakan jim kadan byan ganawarta da shugaban Tunusiyan Beji Caid Essebsi a Tunis babban birnin kasar ta Tunusiya. A cewar Merkel din wadda ta fara wata ziyarar aiki a Tunusiyan, nan gaba za a rinka baje fasfo din masu neman mafakar da basu samu nasara ba cikin mako guda, kana Jamus za ta tallafa musu in sun koma gida fiye da yadda ta ke taimakon su a baya. A nasa bangaren Essebsi ya bayyana yarjejeniyar da suka cimma da wata kyakkyawar matsaya. Matakan da Jamus din ke son dauka kan masu neman mafaka daga Tunusiya dai na zuwa ne biyo bayan harin ta'addancin da wani dan Tunusiyan da ba a amince da bukatunsa na neman mafaka ba ya kai a kasuwar Kirsimeti da ke Berlin fadar gwamnatin Jamus din a watan Disambar bara. Harin da aka danganta shi da tsaikon da aka samu na samun takaddunsa daga mahukuntan Tunusiyan, wadanda za su bayar da damar mai da shi gida.