1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar KTT da Kasar Sudan

June 21, 2004

Hukumar ECHO ta KTT tayi kimanin shekaru goma tana ba da taimako ga kasar Sudan kuma tana daya daga cikin gaggan kungiyoyin dake famar kai taimakon jinkai zuwa ga lardin Darfur dake yammacin Sudan

Masu fama da yunwa da kishrwa a yammacin kasar Sudan
Masu fama da yunwa da kishrwa a yammacin kasar SudanHoto: AP

A hakika dai mazauna lardin Dafur dake yammacin Sudan suna cikin wani mawuyacin hali na kaka-nika-yi game da makomar rayuwarsu, inda suke fama da yunwa da kisriwa da kuma rashin muhallin zama. Kuma a nan ba ma sai an yi batu a game da kiwon lafiyarsu ba. Tun dadewa talakawan lardin ke fama da radadin yakin basasa kuma yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma bata tsinana kome wajen sassauta musu wannan radadi ba, a cewar Ivo Freijsen mai ba da shawara akan manufofin taimakon jinkai ga Kungiyar Tarayyar Turai. Ya kuma kara da cewar:

Lamarin na da sarkakiyar gaske. A bangare guda akwai kyakkyawan ci gaba a arewaci da kuma gabacin Sudan, lamarin da wajibi ne a yi madalla da shi. Amma fa har yau da sauran tafiya. Domin kuwa a daya bangaren akwai yankuna kamarsu Darfur a yammacin kasar, inda al’amura ke dada yin tsamari ake kuma bukatar karin taimako na jinkai.

Yau dai kimanin shekaru biyu ke nan da Ivo Freijsen ke gudanar da aikinsa a kasar Sudan a matsayin mai ba da shawara ga KTT a matakan taimakon jinkai. Ya na sa ido akan irin ci gaban da ake samu bisa manufa. Yana gabatar da rahotanni zuwa shelkwatar kungiyar tarayyar Turai dake Brussels domin bayanin ire-iren taimakon da ake bukata da kuma yawan kudin da ya kamata a tanada domin gudanar da wannan taimako. Ita kanta hukumar taimakon jinkan ta KTT ECHO a takaice, yau shekaru goma ke nan tana mai gudanar da ayyukanta a kasar Sudan, kuma kamar yadda ta nunar ita ce mafi girma a tsakanin kungiyoyin dake gabatar da taimakon jinkai a dukkan sassa na duniya. Ta kan yi hadin kai da sauran kungiyoyin taimako masu zaman kansu kamar Kwamitin Red Kros da Kungiyar Likitoci ta kasa da kasa da sauran kafofin taimako na MDD. Babban abin da ta fi mayar da hankali kansa shi ne taimakon gaggawa, saboda a daidai irin wannan lokaci mutane ba sa iya taimakon kansu da kansu. To sai dai duk da haka a wannan marra da ake ciki yanzun ba wani abin da zata iya tabukawa domin lafar da radadin da makaurata ke fama da shi a yankin Darfur. An kiyasce cewar a cikin ‚yan watanni masu zuwa dubban daruruwan mutane zasu yi asarar rayukansu sakamakon cututtuka da yunwa a wannan yanki. Yara kanana sune suka fi zautuwa. Babban ummal’aba’isin jinkirin da aka samu shi ne haramta kai taimako da gwamnatin Sudan tayi kuma ana kan haka sai ga damina ta karato ta yadda jigilar kayan taimakon zata ta’azzara saboda rashin kyawon hanyoyi. A halin yanzu haka ba wanda ya san tahakikanin yawan mutanen dake zaman tsammanin warrabuka a wannan yanki. A cikin shekaru goma na ayyukanta Hukumar ECHO ta gabatar da taimako na tsabar kudi Euro miliyan 230 a kasar Sudan.