Jaridun Jamus: Dangote ya dauki hankali
September 25, 2026
Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cikin sharhinta ta ce, 'yan sanda a Afirka ta Kudu sun fitar da rahoton farko kan ci gaba da binciken kisan wasu mata guda tara. Jaridar ta ce, tun farko an gabatar da mata biyu da ake zargi masu shekaru 28 da 31 a gaban kotun birnin Johannesburg kan kashe daya daga cikin mamatan. Sannan an saki wani namiji da aka tuhume su tare, 'yan sanda sun sake shi sakamakon rashin wata hujja da ta danganta shi da kisan.
Mutane da dama a kasar ta Afirka ta Kudu sun harzika da irin yanayin da ake fuskanta na irin wannan kisa da aka samu matan da rabin jikinsu a bude, kuma akwai alamun sun fuskanci cin-zarafi. Afirka ta Kudu tana sahun gaba, cikin kasashen duniya da ake samun laifukan kisa. Kuma wani binciken hukumomin Afirka ta Kudu ya nuna cewa, daya cikin mata uku a kasar sun fuskanci cin-zarafi. Yanzu an saka farkon watan Oktoba na 2026, domin ci gaba da sauraron karar kan wannan kisa da ya tayar da hankali a kasar.
Jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi sharhi mai taken an yi zaben majalisar dokokin Maroko, lokacin da matasa suka nuna kosawa da siyasa tare da neman tserewa zuwa kasashen Turai ta hanyar shiga kasar Sifaniya. Tun gabanin zaben majalisar dokokin Marokon matasa suka fusata da tabarbarewar tattalin arzikin kasar, abin da ya haifar da zanga-zanga. Kana kasar tana fama da karancin kayan aiki a asibitoci, baya ga rashin damar ci-gaban matasan. Al'ummar kasar sun kada kuri'unsu a ranar 23 ga watan Satumbar 2026, inda aka ga karancin matasa kan harkokin zaben.
Ita kuma jaridar die Tageszeitung ta fara sharhinta da cewa, 'yan tawaye a Mali suna kara samun galaba kan gwamnatin mulkin sojan kasar. Jaridar ta ce, sojojin Mali sun fuskanci koma-baya a hannun gamayyar 'yan ta'adda masu kaifin kishin addinin Islama na JNIM da kuma 'yan tawayen Abzinawa na FLA. An dai nuna hotunan sojojin da suka mutu, a fafatawar da aka yi a wani gari da ke yankin tsakiyar kasar. 'Yan ta'addan sun yi ikirarin kashe sojojin gwamnati 150 da kama wasu kimanin 90, ciki har da mayakan Rasha biyar.
A nata sharhin jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi, hamshakin mai arzikin Najeriya Aliko Dangote wanda ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka ya zama tamkar Rockefeller wanda ya zama mafi fice tsakanin attajiran Amurka. Kiyasin mujallar Forbes ya nuna cewa, arzikin Dangote a yanzu ya kai dalar Amurka bilyan 52. Dangote na matsayi na 35 a duniya baki daya, kuma mai shekaru 69 a duniyar ya kasance na farko mafi arziki tsakanin kasashen Afirka da tazara mai yawa tsakaninsa da sauran masu arzikin nahiyar.