1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangote zai kaddamar da gina matatar mai a Kenya

September 30, 2026

Ana sa ran, attajiran nan na Najeriya Aliko Dangote zai kaddamar da gina matatar mai a kasar Kenya da darajarta za ta kai dala biliyan 16.

Dangote zai kaddamar da gina matatar mai a Kenya
Hoto: Marvellous Durowaiye/REUTERS

Za a gina matatar man Dangote a Kenya a wani mataki na cimma burin nahiyar Afirka ta dogaro da kanta wajen samar da man fetur. Dangote da dama ya gina matatar mai a Najeriya, ya ce matatar da za a samar a gabashin Afirka a yanzu, za ta rika samar da gangar mai 700,000 a kowace rana, abin da zai sanya ta fi ta nahiyar Turai girma. Za a gina matatar Dangoten a gabar tekun Kenya da ke Lamur, yankin da ke zama cibiyar tashar jiragen ruwan kasar.

Karin bayani: Matatar man Dangote za ta yi tasiri a Kenya?

Tun da fari an kai ruwa rana wajen gina fara aikin gina matatar, inda wadanda da suka yi ikrarin cewa a filinsu za a ginata suka shigar da kara. Ko da yake hukuncin kotu a wannan makon ya ba da damar ci gaba da aikin, sai dai kuma za a ci gaba da zaman shari'a. Haka kuma masu rajin kare mukalli na nuna damuwa kan tasirin gina matatar.