1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Najeriya: Farashin dala na kara hauhawa

November 1, 2022

Kasa da makonni biyu da sanar da shirin babban bankin Tarayyar Najeriya na sauyin fasalin kudin kasar Naira, ana ci gaba da fuskantar tabarbarewar darajar kudin da kusan kaso 20 cikin 100 a tsawon mako guda kacal.

Najeriya | Naira | Daraja | Faduwa | Tattalin Arziki
Darajar kudin Najeriya Naira, na kara tabarbarewaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Ya zuwa yanzu dai ba batun farashi ake cikin kasuwar canji ba, batu ne na in ka gani sayi a karon farko a cikin tarihin canjin. A cikin mako guda kacal farashin dalar Amirka ya tashi daga Naira 730 kan kowace dala ya zuwa nema a rasa. Ana dai ta'allaka wani kace-nace tsakanin babban bankin Najeriyar CBN da ma'aikatar kudin kasar, a matsayin sanadin rushewar da ta mai da kowa zama cikin halin dar-dar. Garba Mati dai ya share sama da shekaru 42 cikin masana'antar canjin kudi ta Najeiryar, kuma a cewarsa bai taba ganin lalacewar da ake fuskanta yanzu ba. Ranar biyan bukata rai ba ya tasiri ko kuma rusa tattalin arzikin al'umma dai, tuni hauhawar farashin ta fara nuna alamun tasiri ga rayuwa da ci-gaban al'ummar kasar.

Dalar Amirka na neman gagara a kasuwar canjin NajeriyaHoto: DW

Saratu Aliyu na zaman shugabar kungiyar kananan 'yan kasuwa na Najeriyar, kuma ta ce tashin dalar ya yi  nisa wajen hargitsa lissafi a kasuwar kasar da ke dogaro da kaya na waje. Kowa ya take shirin ta kaya a tsakanin masu kasuwar da ke ta korafin bacin lisssafi da kuma al'ummar da ke kukan wai-wai dai, daga dukkan alamu 'yan kwanakin da ke tafe na iya kai wa ya zuwa ta'azzarar lalacewar lamura a kasar da ke takama da kayan da ake shigowa da su daga waje. Kama daga tsinken sakace zuwa bukatu manya dai, Najeriyar tai nisa a dogaro da kaya na waje ga rayuwa da walwalar al'umma. To sai dai kuma a fadar  Dakta Isa Abdullahi da ke sharhi kan tattalin arzikin kasar a jami'ar tarraya da ke garin Jos, tashin farashin dalar abu ne na lokaci kankane. 'Yan kwanakin da ke tafe dai, na shirin yin tasiri ga makomar tattalin arzikin kasar da ke kallon hauhwar da babu irinta  a lokaci na yakin neman zabe na siyasa.