Kudin Rubel ya zarta Yuro
May 20, 2022Talla
Kudin na Ruble wanda tsadar man fetur da iskar gas ta sa ya yi tashin gobron zabi a kasuwannin hada-hada na kudi, ya haura da sama da kishi 20 cikin dari a gaban kudin Yuro fiye da lokacin da aka soma yin yakin. A halin a ake ciki kamfanoni da yawa na Turan ya zame musu dole kaunar naki, wajen bin umarnin Putin na yin cinikayyar a Rashar da kudin Rubel. Kudin Rashan shi ne kudin duniya wanda ya fi samun ci gaba fiye da kowanne tun farkon shekara.