Darajar kudin Ruble na Rasha ta hau
March 23, 2022Talla
Putin ya ce, ya bai wa kasashen na Turai wa'adin mako guda, su samar da wani tsarin da za su biyan kudin gas din. da kudin Ruble na Rasha a maimakon kudin Yuro ko Dala da suke biya da shi. Shugaban na Rasha ya bukaci babban bankin Turai da gwamnati da su kafa wani sabon tsari wanda dole ya ƙunshi sayan Ruble a kasuwannin musayar kudi.Wannan sanarwar dai ta yi tasiri nan da nan a kan kudin kasar na Rasha, wanda ya tashi a kasuwannin hannayen jari fiye da kudin Yuro da Dala. Fadar shugaban kasar Ukraine ta yi Allah wadai da yakin tattalin arziki da Moscow take yi don karfafa kudinta na Ruble.