1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Darasin Rayuwa: 18.12.2024

December 20, 2024

Shirin Darasin Rayuwa da ke nazari kan irin darussa da mutane suka koya a al'amuran da suka shafi rayuwarsu na wannan makon ya duba ne kan batun nan na kashe kudin da ya wuce kima wajen gudanar da shagulgular biki.

Darasin Rayuwa: 18.12.2024
Darasin Rayuwa: 18.12.2024Hoto: Environmental Image/IMAGO

Bikin aure, hidima ce da ke bukatar kashe kudi idan a aka dauko shi, sai dai a iya cewa shigowar sabbin al'adu na da alaka da yadda aka fi kashe makudan kudade a lokacin biki a yanzu. Ga misali a baya a kan gudanar da shagalin biki ne a cikin gida, sai dai a yanzu saboda cakuduwar Bahaushe da bakin al'adu a kan yi shagali ne sosai.Daga kasa za a iya sauraron sauti.