1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tir da rikicin Darfur

Ramatu Garba Baba
July 15, 2020

Majalisar Dinkin Duniya tare da Kungiyar tarayyar Afirka, sun yi tir da rikicin yankin Darfur na kasar Sudan da ya yi sanadiyyar rayuka mutum kimanin tara tare da raunata wasu mutum ashirin.

Darfur Munition in Nyala
Hoto: Getty Images/AFP/A. Shazly

Majalisar Dinkin Duniya tare da Kungiyar tarayyar Afirka sun soki matakin son mayar da hannun agogo baya a yankin da ake kokarin ganin an samar da zaman lafiya mai dorewa. Rikicin da ya tayar da hankulan jama'a a yankin Darfur da ke arewacin kasar Sudan din, ya yi sanadiyyar rayukan mutum tara baya ga wasu mutum ashirin da suka jikkata.

Sun baiyana rashin amincewa da yunkurin tayar da hankula a daidai lokacin da gwamnatin wucin gadi da aka samar da kungiyoyi na masu gwagwarmaya ke shirin kulla yarjejeniyar samar da zaman lafiya a kasar.

Yankin na Darfur ya sha fama da rikicin kabilanci inda aka rasa rayuka sama da dubu dari uku baya ga wasu miliyan biyu da rabi da suka rasa matsugunni a tashe-tashen hankula da suka auku a shekarar 2003.