1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daruruwan mutane sun mutu a Kwango

May 7, 2023

Alkaluma na ci gaba da karuwa daga adadin wadanda suka mutu a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, bayan wani ruwan sama mai karfi da aka tafka.

Hoto: REUTERS

Adadin wadanda suka salwanta sakamakon ibtila'in da ya samo asali daga ruwan sama da aka tafka a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, ya zarta mutum 200 a yanzu.

Hukumomin yankin Kivu inda lamarin ya faru, sun ce baya ga wadanda suka mutum akwai ma karin wasu sama da 100 da suka bata.

Kauyuka da dama ne dai a yankin tafkin Kivu suka fuskanci ambaliya, sakamakon ruwan sama kamar da bakin masaki da aka tafka, wanda ya sanya koguna suka yi ta batsewa.

Ruwan har ila yau a cewar mahukuntan yankin ya yi awon gaba da gidaje da dama.

Ko a 'yan kwanakin da suka gabata ma dai sama da mutum 100 ne wani ibtila'in na ruwan sama ya salwantar a wani bangare na tafkin na Kivu da ke makwabtaka da Ruwanda.