Daruruwan mutane sun mutu a Saliyo
August 14, 2017Talla
Rahotannin da ke fitowa daga Freetown babban birnin kasar Saliyo, na cewa ana fargabar mutuwar sama da mutane 300 yayin da wasu sama da 2000 kuwa suka rasa muhalli, sakamakon zaftarewar laka da ta binne daruruwan mutane da safiyar wannan Litinin. Lamarin ya shafi birnin ne da kewaye, inda gidaje masu yawa suka ruguje bayan ruwan sama mai karfi da aka tafka cikin dare.
Wasu ma'aikatan sashen ajiyar gawarwaki na wani asibitin da ke Freetown sun ce yawan gawarwaki sun zarta abin da asibitin zai iya dauka. A halin dai da ake ciki ana nuna matukar bukatar taimako ne na motocin daukar marasa lafiya don aikin ceto. Bayanai sun ce an aike da sojoji don taimaka wa aikin ceton da ke wakana a wajen.