1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIndiya

Akalla fasinjoji 200 sun rasu a hatsarin jirgin saman Indiya

June 12, 2025

Hatsarin ya rusta da Indiyawa 169 da 'yan Burtaniya 53 da 'yan Portugal bakwai da kuma dan Canada daya.

Masu aikin kwana-kwana sun kashe wutar da ta tashi da kuma dakile hayakin da aka rika gani
Masu aikin kwana-kwana sun kashe wutar da ta tashi da kuma dakile hayakin da aka rika ganiHoto: Amit Dave/REUTERS

Wani jirgin sama na kasar Indiya da ya tashi zuwa birnin London dauke da mutane 242 ya yi hatsari da safiyar Alhamis a birnin Ahmedabad da ke arewa maso yammacin Indiyar. Ya zuwa yanzu hukumomi sun tabbatar da mutuwar akalla mutum 204 a hatsarin.

Hotunan da aka yada a gidajen talabijin na kasar ta Indiya sun nuna hayaki na tashi daga wurin da jirgin ya fadi, wuri da kuma ya kasance gidajen mutane da ke kusa da filin jirgin Ahmedabab, gari mai sama da mutum miliyan biyar.

Jirgin dakon kayan DHL ya yi hatsari a Lithuania

Firaministan Indiya Narendra Modi ya nuna kaduwa da hatsarin da ya auku a jiharsa ta Gujarat, tare da bayyana alhinin faruwar al'amarin.

Masu aikin kwana-kwana sun kashe wutar da ta tashi da kuma dakile hayakin da aka rika gani a tarkacen jirgin mai cike da mai kasancewar bai dade da tashi ba daga filinsa.

Shi ma Firaministan Burtaniya Keir Starmer ya ce ya kadu matuka inda ya jajanta wa iyalan wadanda hatsarin ya rutsa da su.

Mutum bakwai sun halaka a hadarin jirgin sama a Mexico

Mutum 169 daga cikin fasinjojin dai Indiyawa ne sai kuma 'yan Burtaniya 53 da 'yan Portugal bakwai da kuma dan Canada daya a cikin jirgin na Boeing 787 da ya tashi zuwa birnin Gatwick  na Burtaniya.

Kamfanin Boeing ya ce ya na tattara bayanai kan hatsarin jirgin sannan zai fitar da rahoto a hukumance a nan gaba bayan ya kammala fahimtar yadda lamarin ya faru.