1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daruruwan sojojin Kenya sun isa Kwango

November 13, 2022

A kokarin murkushe 'yan tawaye M23 a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, kasashen gabashin Afirka na aika dakaru. Kasar Kenya ce ta baya-bayan nan da nata suka isa.

Sojojin gwamnatin kasar KenyaHoto: Brian Inganga/AP/picture alliance

Sojojin kasar Kenya sun sauka a birnin Goma da ke a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, a wani kokari na hada karfi wajen murkushe tawayen kungiyar M23 da ke zama barazana ga zaman lafiya yanzu a Kwangon. A baya-bayan nan dai mayakan tawayen na M23 na zafafa hare-hare a musamman arewacin lardin Kivu, inda suke kama wasu yankuna.

Sama da sojoji 900 ne dai majalisar dokokin kasar Kenya ta amince a aika su zuwa Kwangon, domin shiga cikin dakarun hadin gwiwa na yankin gabashin Afirka da za su yaki rikicin na Kwango. Hukumomin Kenyar sun ce tawagar mayakan kasar za kuma ta yi aiki tare da da wasu kungiyoyin agaji wadanda ke a Kwango domin samar da daidaiton da ake muradin ganin an samu a gabashin kasar.