Daruruwan yan Pakistan sun gudanar da zanga zangar bore ga gwamnati
May 2, 2007Talla
Daruruwan yan Pakistan sun gudanar da wata zanga zanga a kofar kotun kolin kasar dake birnin Islamabad.
Masu zanga zangar na adawane da ci gaba da sauraron shari´ar da akewa daya daga cikin manyan alkalan kasar ne.
Kotun dai na zargin Iftikar Mohd Chaudhry ne da yin wasa da aikin sa, zargi daya kai shugaba Parvez Musharraf dakatar dashi daga bakin aiki.
Wannan mataki dai da shugaban na Pakistan ya dauka a cewar rahotanni na daga cikin batutuwa, da suka jefa kasar ta Pakistan cikin rudani na siyasa.
Duk da cewa anyi arangama a tsakanin masu zanga zangar da kuma yan sanda, ya zuwa yanzu babu rahoton rasa rai, to amma da yawa sun jikkata.