1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Darurwan mutane sun yi zanga-zanga a Senegal

March 3, 2024

Masu zanga-zanga na son a gudanar da zabe kafin karewar wa'adin mulkin shugaban kasar Macky Sall.

Darurwan mutane sun yi zanga-zanga a Senegal
Darurwan mutane sun yi zanga-zanga a SenegalHoto: John Wessels/AFP

Daruruwan mutane sun yi zanga-zangar birnin Dakar na Senegal domin ganin an gudanar da zabe kafin wa'adin mulkin shugaban kasar Macky Sall ya cika a ranar 2 ga watan Afrilun 2024.

Gamayyar kungiyoyin adawa da na yakin neman zabe da suka kira zanga-zangar ce suka bukaci a saki jagoran adawar kasar Ousamane Sonko. Da yawa daga cikin masu boren sun rike hotunan Sonko wanda aka daure bisa zargin haddasa tarzoma tare da kiran Shugaba Sall a matsayin mai mulkin kama karya.

Karin bayani: Senegal: Kokarin shawo kan rikicin siyasa

Kasar da ke yammacin Afirka ta fada cikin rikicin siyasa ne bayan da shugaban Sall ya dage babban zaben kasar da aka shirya gudanarwa a ranar 25 ga watan Fabarairu da ya gabata. Taron warware rikcin da 'yan adawa suka kauracewa a makon da ya gabata, ya bukaci a gudanar da zaben kasar a ranar 2 ga Yunin wannan shekarar.