1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An daure jagoran tsagerun Sudan

Suleiman Babayo AMA
December 9, 2025

Kotun duniya mai hukunta manyan laufukan yaki ta dauke jagoran tsagerun Janjaweed na Sudan a gidan fursuna saboda rikicin lardin Darfur.

Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman jagoran tsagerun Janjaweed na Sudan
Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman jagoran tsagerun Janjaweed na SudanHoto: Peter Dejong/ANP/picture alliance

Kotun duniya mai hukunta manyan laifukan yaki da ke birnin Hague na kasar Netherlands ta yanke hukuncin daure shekaru 20 a gidan fursuna ga jagoran tsagerun kungiyar Janjaweed na Sudan, bisa laifukan yaki da aka yi kan al'ummar yankin Darfur a shekaru fiye da 20 da aka kwashe ana tarzoma.

Yanke hukuncin

Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman jagoran tsagerun Janjaweed na SudanHoto: Peter Dejong/ANP/picture alliance

Shi dai Ali Muhammad Ali Abd_Al-Rahman tun watan Oktoba aka same shi da laifuka 27 da aka tuhume shi.

Jagoran tsagerun Ali Abd_Al-Rahman ya taka muhimmiyar rawa a rikicin Darfur tsakanin shekara ta 2003 zuwa 2004 lokacin da mayakan suka aikata laifukan yaki kan dan Adam. Masu gabatar da kara a kotun ta duniya sun bukaci daure jagoran tsagerun na tsawon rai da rai, ganin irin rawar da ya taka a rikicin na Darfur da ke yammacin kasar Sudan.

A shekara ta 2005 Kwamitin Sulhu na Majaisar Dinkin Duniya ya bukaci kotun duniya mai hukunta laifukan yaki ta gudanar da bincike domin hukunta masu hannu bisa laifukan yaki a rikicin na Lardin Darfur da ke Sudan.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Babban labarin DW

Babban labarin DW

Tsallake zuwa bangare na gaba Karin labarai daga DW