Turkiyya: Kotu ta yanke hukunci kaso ga Bajamusa
November 14, 2018A kasar Turkiyya, wata kotun birnin Edirne na Arewa maso yammacin kasar ta yanke a wannan Laraba hukuncin zaman kaso na tsawon shekaru shida da watanni uku ga wata mata Bajamusa mawakiyar Kurdawa da ke da zama a birnin Kolon a bisa samunta da laifin kasancewa mamba ga kungiyar ta'adda.
A ranar 23 ga watan Yunin da ya gabata ne dai mahukuntan Turkiyyar suka kama matar mai suna Saide Inac da aka fi sani da Hozan Cane a daidai lokacin da take rakkiyar jam'iyyar HDP mai kusanci da jam'iyyar PKK ta Kurdawa a lokacin yakin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da Turkiyyar ta shirya a ranar 24 ga watan Yuni da ya gabata.
Sai dai lauyenta Mustafa Peköz ya ce zai daukaka kara. Yanke wa wannan Bajamusa hukuci na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Turkiyya da Jamus suka soma kyautata dangantakarsu wacce ta fuskanci komabaya a watannin da suka gabata.