An bude taron tattalin arziki a birnin Davos
January 21, 2020A jawabin da ta gabatar a zauren taron shahararriyar matashiyar nan mai fafutukar kare muhalli Greta Thunberg ta bayyana rashin gamsuwarta da yadda ta ce har yanzu babu wani abin a zo a gani da kasashen duniya suka yi wajen kare muhalli duk da taruka da ake ta gudanarwa kan batun matsalar sauyin yanayin da ma makudan kudin da kasashe da kamfanoni ke ikirarin kashewa. Sai dai daga nashi bangare Shugaba Donald Trump na Amirka ya yi gugar zana ga 'yan fafutukar kare muhallin, wadanda ya kira da 'yan mugun fata ga makomar muhallin duniya da yada labaran karya kan tashin duniya. Trump ya kuma bayyana cewa yana alfahari da yadda tattalin arzikin Amirka ke kara bunkasa fiye da yadda duniya ke tsammani. A bara dai Trump bai jima a wajen taron ba ya kama gabansa, sai dai a wannan karon ana tsammanin zai gana da shugabannin wasu kasashe da suka hadar da Iraki da Pakistan a gefen taron.