1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

DAVOS: Ukraine ta jaddada bukatar shiga NATO

January 16, 2024

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya gabatar da bukatu guda biyu a taron tattalin arziki na Davos, inda ya nemi karin kudi da makamai don tunkarar kasar Rasha, da kuma shigar da kasar kungiyar tsaro ta NATO.

Shugaba Zelensky na Ukraine da Klaus Schwab da ke shugabantar taron Davos
Shugaba Zelensky na Ukraine da Klaus Schwab da ke shugabantar taron DavosHoto: Manuela Kasper-Claridge/DW

Yayin da ministan harkokin wajen Saudiyya ya caccaki Isra'ila a taron tattalin arzikitattalin arziki na duniya wato Davos da cewa, tana jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin hatsari, shi kuma shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky, ya jaddada bukatar shiga kungiyar tsaro ta NATO a wannan shekara ta 2024.

Zelensky, ya sanar da sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg, cewar yana bukatar kungiyar ta gaggauta daukar mataki a wannan shekara na matso da muradun Ukraine shiga kungiyar.

Ya kuma bayyana halin da kasar ke ciki a yakin da suke fafatawa da Rasha, tare da bukatar karin tallafin kayayyakin yakin soji ga Ukraine musamman domin maida martani kan hare-haren Rasha ta sama a wasu sassan kasar.