1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Me ya hana magance rikicin Sudan?

Mouhamadou Awal Balarabe SB
May 29, 2026

Fara dawo da 'yan Ghana daga Afirka ta Kudu sakamakon cin zarafin da 'yan Afirka ke fuskanta a Afirka ta Kudu da yaduwar cutar Ebola gami da rikicin Sudan sun dauki hankalin jaridun Jamus.

Sudan El-Fasher 2025 | Rikicin Sudan
Rikicin SudanHoto: Rapid Support Forces (RSF)/AFP

Sharhin da die Tageszeitung ta yi mai taken "Ghana ta kwashe 'yan kasarta daga Afirka ta Kudu" sakamakon kyama da ake nuna musu, inda jaridar ta ce fadar mulki ta Accra ta fara mayar da 'yan kasarta da ke zaune a Afirka ta Kudu gida saboda zanga-zangar adawa da tsarin shige da fice ba bisa ka'ida ba.

'Yan Ghana da suka dawo daga Afirka ta KuduHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Tun watan Afrilu ne, kungiyar "March-March" ta fara shirya zanga-zangar da nuna adawa da baki marasa takardu a manyan biranen kamar Pretoria, Johannesburg, da Durban.

Die Tageszeitung ta ce kungiyar na neman gwamnatin Afirka ta Kudu ta sanya ka'idojin biza masu tsauri tare da gyara manufofin neman mafaka, da kwaskware matakan daukar 'yan ci-rani marasa takardu aiki.

'Yan Ghana da suka dawo daga Afirka ta KuduHoto: Siphiwe Sibeko/REUTERS

Jaridar ta kara da cewar wasu 'yan Ghana sun shafa wa kansu ruwa inda suke nemi hukumomin kasarsu mayar da su gida, lamarin da Accra ta saurara da kunnuwan basiri inda ta mayar da rukunin farko na 'yan kasar Ghana 300 gida. 

A cewar jakadan Ghana a Afirka ta Kudu, Benjamin Quashhie, kimanin 'yan kasar Ghana 890 sun yi rijista don a mayar da su gida.

Rikicin Sudan

Cin zarafi a rikicin SudanHoto: Human Rights Watch

A nasu bangaren jaridun Frankfurter Allgemeine Sonntagszeitung da Faz.Net sun dasa ayar tambaya kan yakin basasa na Sudan.

Jaridun suka ce kasar na fuskantar bala'in jin kai mafi muni da aka taba fuskanta a wannan karni, kuma yakin na shafar kasashen Yamma amma kai kai mizanin sauran yake-yake ba. Kuma abin bakin cikin ma babu rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, in ji Faz.Net.

Jaridun sun kara da cewa, shekaru uku ke nan da rikici ya barke ​​a babbar kasar ta gabashin Afirka, amma babu wanda ya sa lokacin da za a kawo karshensa.

Rikicin SudanHoto: Mohammed Nzar Awad/Anadolu/picture alliance

Alhali a tsakiyar watan Afrilu, fitillu sun sake kunnuwa a Sudan lokaci da aka gudanar da wani taro a Berlin, inda aka yi alkawarin bayar da tallafi Euro biliyan daya da rabi.

Amma taron bai lalubo hanyar fita daga rikicin ba, duba da cewa ba a gayyaci bangarorin da ke yakin ba, wato dakarun gwamnati Sudan da rundunar ko-ta-kwana ta RSF ba.

Cutar Ebola ta dauki hankali

Taimakon hukumar lafiya WHO kan yaki da cutar EbolaHoto: Andrew Kasuku/AP Photo/picture alliance

Ita kuwa Zeit Online ta mayar da hankalinta ne kan mummunan hali da cutar Ebola ta jefa Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, inda ta ce tsohon ministan kiwon lafiya na Jamus Karl Lauterbach ya yi kira da a kara taimakon raya kasa bayan barkewar cutar Ebola.

Jaridar ta ce bai kamata Jamus ta rage tallafin da take ba wa Kwango ba, domin in ba haka ba kwayoyin cuta kamar Ebola na iya yaduwa tare zama annoba.

Zeit Online ta ce katse tallafin raya kasa da Amurka ta yi ya sa tsarin kiwon lafiya na kasashen Afirka kamar Jamhuriyar Dimukuadiyyar Kwango ya dada lalacewa.

Yaki da cutar EbolaHoto: Badru Katumba/AFP

Idan ita ma Berlin ta dauki mataki mai kama da haka, wannan zai iya bai wa kwayoyin cuta masu hadari kamar Ebola yaduwa cikin hanzari, kuma su zama annoba tare da ja wa kasashen Turai komabayan tattalin arziki.

Tsohon Minista Lauterbach da ma jaridar sun yi gargadi game da abin da suka kira "tarin 'yan gudun hijira daga kasashen Afirka zuwa Turai," da cutar Ebola za ta iya haifarwa sakamakon lalacewar tsarin kiwon lafiya.

Ebola ta barke ne a tsakiyar watan Mayu a  Kwango, inda kawo yanzu akalla mutane sama da 900 suka kamu da ita, yayin da ta kashe mutane sama da 200.

Dangantakar ma'adanai tsakanin Afirka da Turai

Welt online ta mayar da hankali kan alakar arziki tsakanin Afirka ta Turai, inda ta ce "Kungiyar Tarayyar Turai na neman dogaro kan sabbin hanyoyi wajen jigilar ma'adinai da sauran kayayyaki masu amfani da take bukata daga Afirka."

Ma'adanan Afirka suna da tasiri ga harkokin ci-gaba a duniyaHoto: Adrian Kriesch/DW

Jaridar ta ce ana gina sabon layin dogo a tsakinin kasashen da ke da arzikin ma'adinai na Afirka. Wannan na iya zama babbar dama  ga Turai, kuma barazana ga abokiyar hamayyarta China.

Welt online ta ce duk abin da kasashen Yamma ke bukata a fannin makamashi, ana samunsu a yankunan da ke da arzikin albarkatun kasa na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da Zambiya da Angola.

An yi niyyar shunfuda sabuwar hanyar jirgin kasa ne don jigilar muhimman albarkatun kamar jan karfe, da cobalt, da lithium, da coltan, da nickel zuwa Turai. Saboda hake ne a lokacin ziyararta a China, ministar tattalin Arziki ta Jamus Katherina Reiche ta yi kira da a samar da ingantacciyar hanya da kuma yanayin kasuwa mai adalci ga muhimman albarkatun kasa masu daraja.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani