1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Denis Nguesso ya sake lashe zaben shugaban Congo-Brazaville

March 18, 2026

Shugaban kasar Congo-Brazaville, Denis Sassou Nguesso, ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasa karo na biyar a jere, kamar yadda sakamakon wucin gadi ya nuna.

Shugaba Denis Sassou Nguesso na Kwango-Brazzaville
Shugaba Denis Sassou Nguesso na Kwango-BrazzavilleHoto: Russian Foreign Ministry Press Service/TASS/dpa/picture alliance

Ministan harkokin cikin gida, Raymond Zephirin Mboulou, ya bayyana cewa Nguesso ya samu kashi 94 da digo 82 na ƙuri’u, inda ya doke sauran ‘yan takara shida da suka fafata da shi.

A yayin zaɓen, an katse intanet a faɗin ƙasar, tare da takaita zirga-zirga a babban birnin Brazzaville. Duk da rahoton cewa kashi 84 cikin ɗari na masu kaɗa ƙuri’a sun fito, wasu wuraren zaɓe sun kasance babu cunkoso, inda wasu ‘yan ƙasa suka ce ba sa ganin za a samu sauyi a shugabanci.

Wannan zaɓe na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin wasu tsofaffin shugabannin Afirka na ci gaba da riƙe madafun iko, inda Nguesso ke cikin waɗanda suka fi dadewa a mulki, bayan shugabannin Cameroon da Equatorial Guinea.