1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 70 da kafa tashar Deutsche Welle

Christoph Strack ATB/LMJ
May 10, 2023

Shekaru 70 da suka gabata, aka kaddamar tashar Deutsche Welle a matsayin kafar yada labarai ta kasa da kasa. A lokacin ana fama da yakin cacar-baka, sai dai a yanzu ma ana fama da tarin kalubale a duniya.

Deutsche Welle | Shekaru 70
Deutsche Welle ta cika shekaru 70 da kafuwa

An kaddamar da tashar Deutsche Welle a matsayin kafar yada labarai ta kasa da kasa, shekaru 70 din da suka gabata. lokacin ana fama da yakin cacar-baka, sai dai a yanzu ma ana fama da tarin kalubale a duniya. A ranar uku ga watan nan na Mayu ne tashar ta Deutsche Welle ta cika shekaru 70 cif da kafuwa, kuma ta fara ne a matsayin kafar yada labarai ga kasashen waje. Yuri Rescheto dan asalin kasar Rasha, na daga cikin ma'aikatan tashar ta DW. A cewarsa jan tambarin da aka buga a fasfo dinsa na sahalewar fita daga Rashan, ya share masa fage.  Rescheto da ke zaman shugaban sashen Deutsche Welle a Moscow, ya ketara kogin da ya raba birnin Ivangorod na Rasha da birnin Narva na Estonia ta wata doguwar gada. A matsayin ma'aikacin tashar Jamus din DW na karshe da ke aiki a Rasha, ya bar kasar da ta haramta masa aikinsa da ma kafar yada labaran da yake yi wa aiki. Ga fadar Kremlin tashar DW wakiliya ce da ta hada baki da kasashen waje. Kuma misalai daga takwarorinmu da ke aiki a Rasha, na nuni da cewar kafofin yada labarai na fuskantar matsin lamba a duniya baki daya ciki har da DW.

Karin Bayani: Ra'ayoyin masu sauraron Deutsche Welle daga Yamai, Nijar

Matsin lamba kan 'yancin yada labarai ya gawurta, kuma wannan shi ya sa aikinmu  yake kara zama mai matukar muhimmanci a cewar shugaban tashar DW Peter Limburg. Da aka tambaye shi shekaru 70 da kafuwar tashar DW idan za ka yi waiwaye a zamaninka a DW wadanne nasarori za ka ce an cimma? Peter Limbourg ya ce akwai nasarori da dama. Kuma yana tsammanin abubuwan alheri sun faru ga Deutsche Welle. Ya kara da cewa an samu nasarar kara yawan kasafin kudi da ma shawo kan kalubalen fasahar zamani na digital, baya ga fayyace dalla-dalla dabaru da hikimomin tsarin gudanarwar aiki. A cewar Limburg DW ta kasance kafar yada labarai ta duniya da ta mayar da alkiblarta kan masu sauraro da masu bibiyar ta a kafofin sada zumunta, kuma ya gamsu kwarai da dukkan abubuwan da abokan aiki suka cimma domin babu shakka aikin ya zama mai matukar muhimmanci a 'yan shekarun baya-bayan nan. Sai dai kuma akwai kalubalen da ake fuskanta yanzu haka na yaki a nahiyar Turai, inda matsin lamba kan 'yancin 'yan jarida da kafofin yada labarai da ke karuwa wanda hakan ya nsaya aikin ke kara zama mai muhimmancin gaske.

Shugaban tashar DW Peter LimbourgHoto: DW

Shekaru 70 da suka wuce tashar Deutsche Welle ta fara yada labarai da kamalai masu karfafa zukata na shugaban kasa Theodor Heuss a ranar uku ga watan Mayu na shekara ta 1953 yana mai cewa: "Ya masu sauraron mu daga kasashen da ke nesa." Wadannan kalamai da su aka bude shiri da ke nuna aniyar bai wa masu sauraro da ke kasashen waje bayanai na siyasa da tattalin arziki da kuma al'adun Jamus. A matsayin tasha mai gajeren zango, DW an kafa ta ne a Cologne kuma daga nan take kai wa ga masu sauraro a sassa da dama na duniya. Da farko an fara yada shirin ne da harshen Jamusanci kadai, sannan sauran harsuna na kasashen waje aka kara su a 1954. Tashar talabijin ta biyo baya a 1992, daga bisani kuma aka shigo da kafar online wato yada shirye-shirye ta Internet. Sai dai kuma yada shiri ta gajeren zango tuni zamaninsa ya shude. Shugaban tashar Deutsche Welle Peter Limburg ya ce a yau kafofin yada labarai sun dogara ne a kan Internet da kafar sadarwar zamani na Social Media da kuma tashoshi abokan hulda.

Karin Bayani: "An yi wa Deutsche Welle canje-canje masu yawa a tsukin shekaru 60"- Umaru Aliyu

Limburg ya shafe shekaru tara da rabi yana jagorantar tashar Deutsche Welle, ya kuma jaddada muhimmancin tashar a kasashen ketare. A cewarsa yana tsammanin aikin jarida a kasashen ketare yana fuskantar babban kalubale kuma ya kamata tashar ta ci gaba da isa ga al'umma, saboda masu mulkin kama-karya a duniya na kokarin toshe hakan a wasu lokutan, da ma yin tarnaki wannan shi ne barazanar da aikin jarida na kasa da kasa yake fuskanta. Limburg ya kara da cewa ma'aikata su ne ginshikin nasarar Deutsche Welle kamar yadda kudirin tashar ya nunar. Ma'aikata kimanin 3,700 daga kasashe fiye da 60 a fadin duniya, ke aiki a cibiyoyin tashar da ke Bonn da Berlin. Wannan ya nuna tashar ta hada al'umomi mabanbamta fiye da kowace kafar yada labarai a Jamus. Haka kuma an kara yawan wakilai masu aiko da rahotanni daga Afirka da Asiya da kudancin Amirka a 'yan shekarun baya-bayan nan.