1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dharmendra: Babban bango ya fadi a Bollywood

Abdul-raheem Hassan MAB
November 25, 2025

Duniyar fina-finan Bollywood ta yi rashin babban jigo, jarumin da ya fito a fiye da fina-finai 300. Dharmendra mai shirya fina-finai da ya rikide zuwa siyasa ya kwanta dama bayan shafe sama da shekaru 60 yana fafatawa.

Marigayi jarumi Dharmendra a lokacin da ya yi bikin cika shekaru 80 da haihuwa
Marigayi jarumi Dharmendra a lokacin da ya yi bikin cika shekaru 80 da haihuwaHoto: AFP

An haifi Dharmendra a cikin iyalin Jat Sikh a jihar Punjab a ranar 8 ga watan Disamban 1935. Amma ya tsallaka zuwa Mumbai a farkon shekarun 1960 domin gwada sa’arsa a fim, inda ya fara fitowa a fina-finai na soyayya da na tausayi. Salonsa na daban da kuzari da kwarewarsa suna ba shi damar zama jarumi cikin sauri a shekarun 1960 zuwa 1970.

Jarumin ya fito a wasu fina-finai kamar Bandini a 1963 da fim "Anupama" na 1966 wanda ya nuna tsantsar tausayi. Sai kuma fim "Phool Aur Patthar" da aka yi a 1966 da ya daga sunansa sosai.

Fim "Mera Gaon Mera Desh" na shekarar 1971 ya nuna bajintar iya fada, sai fim "Sholay" na shekarar 1975 inda ya taka rawar Veeru, daya daga cikin fina-finan mafi shahara a tarihin Bollywood. Sai fim "Chupke Chupke" na 1975, ya taka rawar barkwanci. Wadannan fina-finan sun tabbatar da kwarewar Dharmendra  a fagen jarumta da barkwanci da soyayya.

Takaddamar aurensa da batun addini

Rayuwar Dharmendra ta shiga kafofin watsa labarai sosai lokacin da ya fara soyayya da fitacciyar jaruma Hema Malini, sakamakon yana da aure da matasarsa ta farko Prakash Kaur kafin ya fara nemanta. Amma duk da haka, sun yi aure da Hema a 1980 wanda ya haifar da cece-kuce a kafafen yada labarai har ma a cikin masana'antar.

Jaruma Hema Malinii ce ta kasance matar Dharmendra biyuHoto: Azhar Khan/NurPhoto/IMAGO

An yada jita-jitar cewar Dharmendra da Hema sun canza addini daga Hindu zuwa Musulunci don su auri juna, amma dukkansu sun karyata hakan a fili. Dharmendra ya sha bayyana cewa bai taba sauya addininsa (Hindu) ba, kuma ba a samu wani tabbaci game da jita-jitar ba. Duk da haka, lamarin ya zama daya daga abubuwan da suka yamutsa hazo a tarihin Bollywood. Sai dai kona gawar jarumin bayan mutuwarsa ya kawo karshen shakku kan addininsa.

Gudunmawar Dharmendra a Bollywood

Dharmendra ya fito a fina-finai fiye da 300, kuma ya taka muhimmiyar rawa a kafa salon jarumai masu karfi amma masu tausayi. Jarumin ya fadada komarsa daga jarumi zuwa harkar shiryawa, inda ya tallafa wa sabobbin jarumai, sannan daga baya ya koma fitowa a matsayin uba ko dattijo a fina-finai.

Lambobin yabo da ya samu a rayuwarsa

Padma Bhushan, ya kasance daya daga manyan lambar yabo na gwamnati da ya samu. Sannan ya samu lambar girmamawa ta Film fare don gudummawar rayuwa. Baya ga fim, ya yi takarar siyasa har ya zama dan majalisa na dan lokaci a siyasar Indiya.

Ribar kafa da Dharmendra ya bari a Bollywood

DharmendraHoto: Sujit Jaiswal/AFP

Za a iya cewa Dharmendra ya kafa daula a masana'antar shirya fina-finan Indiya. 'Ya'yansa da suka suka taka rawa sun hada da Sunny Deol, da ya yi fice a fina-finan fada. Sannan yana bayar da umarni kuma dan siyasa ne. Bobby Deol jarumi ne da ya yi fice a shekarun 1990 kuma ya sake yin tashe a baya-bayan nan bayan daina jin duriyarsa na stawon shekaru uku saboda rashin saka shi a aiki. Ya ma taba cewa "Na hakura" yayin tattaunawa a shirin "Koffee with Karan". Sai kuma Esha Deol 'yar Hema Malini, da ta yi fice a fina-finan shekarun 2000.

Da me za a tuna Dharmendra ?

Marigayi Dharmendra ya mutu a ranar 24 ga watan Nuwamban 2025 yana shekaru 89 bayan fama da cutar sarkewar numfashi, amma duk da haka zai ci gaba da kasancewa a zukatan mutane saboda hada karfin jarumta da tausayin halayya da iya barkwanci da zallar iya soyayya.

Dharmendra ya taka rawa a fina-finan da suka zama alama a tarihin Bollywood. Yana cikin jaruman da suka hada tsohuwar Bollywood da sabuwar zamani, kuma tasirinsa yana ci gaba da bayyana ta hanyar 'ya'yansa da fina-finan da ya bari.