FimIndiya
Jarumin fim din Indiya Dharmendra ya rasu
November 24, 2025
Talla
Dharmendra ya rasu a Mumbai a wannan Litinin din bayan tsawon makonni yana kai komo a asibiti.
Dharmendra wanda ya shafe fiye da shekaru 60 yana tashe, ya yi fice a wasu fitattun fina finai tsakanin shekarun 1970 zuwa 1980.
Ya yi fina finai fiye da 300 da suka hada Spaghetti Western-Style da Sholay a 1975 da kuma wani wasan kwaikwayo na soyayya Chupke Chupke a 1975 da "Mera Gaon Mera Desh" a 1971
Ya yi fina-finai masu armashi da Hema Malini inda suka rika fitowa a fina finai da dama kafin daga bisani su yi aure a 1980.