1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTunusiya

Tunusiya: Dimukuradiyya ko kama-karya?

September 9, 2024

Yayin da al'ummar Tunisiya ke shirin kada kuri'a a zaben shugaban kasa na watan Oktoba da ke tafe, tuni manazarta ke nuna damuwa kan irin tarnakin da tsarin dimukuradiyya ke fuskanta a kasar.

Tunusiya | Zabe | Kama-Karya | Kais Saied
Shugaban Tunusiya Kais SaiedHoto: Chokri Mahjoub/ZUMA Wire/IMAGO

Tuni lamura suka yi nisa wajen shiriye-shiryen zaben shugaban kasa na ranar shida ga watan Oktoban da ke tafe a Tunusiya, inda masu nazari kan harkokin kasar ke nuna damuwa da irin matakan kama-karya da Shugaba Kais Saied ke dauka, na dakile tsarin dimukuradiyya a kasar da ke yankin Arewacin Afirka. Daga cikin 'yan mutane 17 da suka bayyana aniyyar tsayawa takarar neman shugabancin kasar, 14 daga cikinsu ko dai an kama su ko kuma aka haramta musu tsayawa duk da umurnin kotu na neman sake dawo da wasu cikin 'yan takara. Hukumar zaben kasar ta amince da takarar mutane uku daga cikin daukacin 'yan takarar, kuma ita kanta ana ganin ta zama sai yadda shugaban kasar ya yi da ita. Ita dai hukumar zaben ta amince da takardun Shugaba Kais Saied na kasar ta Tunisiya, a matsayin dan takara a zaben. Shi ma tsohon dan majalisar dokoki Zouhair Maghzaoui gami da dan kasuwa Ayachi Zammel da ya kafa wata karamar jam'iyya mai muradin kare tsarin jari hujja, takardunsu sun samu tsallake siradin hukumar zaben da Tunusiya.

Dan takarar adawa daga People's Movement ta Tunusiya jam'iyyar Zouhair MaghzaouiHoto: Yassine Gaidi/AA/picture alliance

Koda yake daga bisani 'yan sanda sun cafke dan kasuwan Zammel kan zargin saka hannu na bogi, domin cika sharadin tsayawa takara a zaben na shugaban kasa. Ga mutane irin Hamza Meddeb na Cibiyar Kula da Harkokin Gabas ta Tsakiya da ke birnin Tunis na Tunisiya, na da ra'ayin cewa yanayin da ake ciki ya nuna irin girman matsalar da Tunisiya ke fuskanta wajen tauye tsarin dimukurdiyya a kasar. Masanin ya kara da cewa halin da ake ciki, ya kawar da nasarar da kasar ta Tunisiya ta samu lokacin juyin-juya halin shekara ta 2011 da ya kawo karshen tsarin kama-karya na gwamnatin Marigayi Zine el-Abidine Ben Ali. Shi dai Shugaba Saied na Tunisiya mai shekaru 66 a duniya tsohon malamin koyar da nazarin dokokin kasa, ya dare kan madafun ikon kasar a shekara ta 2019 lokacin da ya lashe zabe da kimanin kaso 72 cikin 100 na kuri'un da aka kada. Tun shekara ta 2021, ya fara daukar matakan karfafa mulkinsa da ake wa kallon na kama-karya.