1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dimuwar iyaye kan turjiyar wasu 'yan matan Chibok

May 9, 2017

Wasu daga cikin sauran 'yan matan sekandaren Chibok da Kungiyar Boko Haram ta sace kuma ta yi garkuwa da su sama da shekaru uku sun nuna turjewa a kokarin cetosu, batu da ya jefa iyaye cikin damuwa.

Nigeria freigelassene Chibok Mädchen in Abuja
Hoto: picture-alliance/dpa/O. Gbemiga

Yayin da wasu daga cikin sauran 'yan matan sekandaren Chibok da Kungiyar Boko Haram ta sace kuma ta yi garkuwa da su sama da shekaru uku da suka shude suka turje wa kokarin cetosu daga hannun Kungiyar, iyaye da 'yan uwan wadannan 'yan mata sun shiga halin damuwa.


Akwai kimanin sauran 'yan mata 115 da yanzu haka ake zaton suna hannun mayakan Boko haram bayan da aka samun nasarar karbo guda 21 a watan Oktoba da kuma wasu guda biyu da suka tsere daga hannun da kuma na baya-bayan nan da guda 82 da aka karbo.


Sai dai rahotanni sun nuna cewa akwai wasu daga cikin 'yan matan da suka nemi ci gaba da zama da mayakan Kungiyar maimakon dawowa gaban iyaye da 'yan uwansu bayan da aka samu damar yin hakan.


Wani daga cikin masu shiga tsakani mai suna Zanna Mustapha shi ne ya tsegunta wa manema labarai cewa akwai 'yan matan daga cikin dalibai makarantar sekandaren Chibok da suka ki amincewa a cetosu daga hannun mayakan Boko Haram yayin da ake tattauanawa tsakanin kungiyar da gwamnatin Najeriya.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani