1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Direbobin manyan motoci a Kamaru sun janye yajin aiki

December 6, 2024

Direbobin sun shiga yajin aikin ne a watan Nuwamba bayan sun zargi sojojin Wagner da kashe musu abokin aiki.

Manyan motoci sun rika fita da mutane zuwa Kamaru a yayin rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
Manyan motoci sun rika fita da mutane zuwa Kamaru a yayin rikicin Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: Rebecca Blackwell/AP Photo/picture alliance

Direbobin manyan motoci da ke dakon kaya tsakanin kasashen Kamaru da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun amince da janye yajin aiki da suka shiga a tsakiyar watan Nuwamban 2024.

Masu dakon kayan sun tsunduma yajin aikin ne bisa zargin sojojin haya na Wagner da harbe abokin aikinsu kamar yadda suka shaida wa kamfanin dillancin Labarai na AFP.

Kamaru ta hana magana kan rashin lafiyar Paul Biya

Duk da wannan yarjejeniyar da mahukunta suka cimma da direbobin, sun fada cewa har yanzu ba su gama gamsuwa da tabbacin tsaron da aka basu ba a kan hanyoyin da suke bi.

An harbe direban ne a yayin da yake shigar da kaya zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da ta dogara ga manyan motoci wajen shigar da kaya saboda rashin teku.

Halin kunci a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

A cewar cibiyar cinikayya ta duniya kashi 40% na kayan da kasar ta yi amfani da shi a shekarar 2022 daga makwabciya Kamaru aka kaimata su ta hanyar amfani da manyan motocin dakon kaya.