Djukanovic ya lashe zaben Montenegro
April 16, 2018Talla
Daga cikin 'yan takara shida na gaba da ke zama baban dan adawa ga Djukanovic wato Mladen Bojanic shi ne ya kasance na biyu da sakamako kashi 33.4 cikin dari kamar yadda sakamakon da hukumar zaben kasar ta bayyana a wannan Litinin a Podgorica babban birnin Montenegro.
Wannan nasara dai za ta ba wa Djukanovic dan shekaru 56 daga jam'iyyar 'yan gurguzu ta DPS mai mulki damar komawa bakin aiki bayan ritaya daga ofishin da ya mulka daga 1998 zuwa 2002.