Dokar aikin kungiyoyin addinai a Kenya
January 20, 2016A kasar Kenya gwamnatin kasar ce ke kokarin ta fito da wata sabuwar doka wacce ta tanadi sanya idanu da tilastawa limaman biyan kudaden gabatar da wa'azi a kafafen yada labarai dama tabbata da sun mallaki takardan shedar samun horon wa'azi daga cibiyoyin koyar da harkokin adinai. Kana dokar na cewa tilas kungiyoyin adinan su yi register.
Ana adawa da dokar aikin kungiyoyin addinai a Kenya
Philip Anyolo daya ne daga cikin shugabannin Cocin katholika, wanda a yanzu haka ke da mabiya sama da miliyan sha hudu a duk fadin kasar.
"Abin akwai matukar kaduwa da mamaki, ganin yadda gwamnati ke yunkurin samar da doka, wacce idan ta tabbata to fa tilas za ta yi illa ga harkokin yada bishararsu. Wannan dai ba daida ba ne kirkiro da doka da ke sanya idanu a kan yadda 'yan kasar kenya ke ibadunsu, wannan dai ya nuna karara yadda aka sa kafa a ka yi watsi da kundin mulkin tsarin kasar."
Goyon bayan dokar aikin kungiyoyin addinai a Kenya
Ganin dai yadda wannan dokar ke cigaba da daga jijoyin wuya a tsakanin shugabinnin addinan kirsta daban-daban, to amma Rev. Sammy Wainaina na Cocin Angilika a kasar Kenyan, na ganin akwai bukatar a yi wa sabuwar dokar kallo da idon basira.
"Zan yi matukar na'am da wannan takunkumi, ya kamata a samu cibiya da za ta hada kungiyoyin addinai, majami'u da masallatai harma sauran kungiyoyi masu zaman kansu a karkashin inwa guda. Domin kuwa dukkaninmu al'umma muke wakilta."
Shugaban kenya ya kare dalillansu na daukar dokar
A nasa bangaren shugaban kasar Kenyan Uhuru Kenyatta, na da yakinin cewar wannan sabuwar doka za ta taka muhimmiyar rawa wajen taka birki ga baza gurbin masu wa'azi a lungunan kasar da ke shiga rigar addini.
"Da akwai masu aikin boge, da ke fakewa da kalmar Allah suna azurta kawunansu ta hanyar amshe kudaden al'umma. Dan haka ya zama wajibi mu samo mafita dan fida irin wadannan mazambata a kusa da mu."
A yanzu dai wannan batu na sabon kudurin da zai sanya takunkumi ga shugabannin addinai a kasar Kenyan shi ke zama abin mahawara ga yawancin 'yan kasar.