1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Biden ya saka hannu kan dokar auren jinsi

Abdourahamane Hassane
December 14, 2022

Shugaban Amirka Joe Biden ya sanya hannu kan dokar yin auren jinsi da ake kira mutunta aure" a wani biki da aka yi a gaban fadar White House a birnin Washington.

USA | Präsident Joe Biden unterzeichnet den Respekt für Ehegesetz
Hoto: Andrew Harnik/AP Photo/picture alliance

Da yake magana a gaban dubban mutane yan kungiya masu fafutukar kare hakin 'yan luwadi da 'yan madigo. Shugaban ya ce dokar wani muhimmin mataki ne na daidaito, 'yanci da adalci ga kowa da kowa. kashi 70 cikin 100 na Amirkawa suna goyon bayan auren 'yan luwadi, amma masu ra'ayin 'yan mazan jiya masu rike da addini na adawa da dokar.