SiyasaThailand
Dokar auren jinsi ta fara aiki a Thailand
January 23, 2025Talla
Ma'aurata na farko 'yan luwadi maza sun yi shagali aurensu a kasar Thailand. Sarkin Thailand ya rattaba hannu kan dokar auren jinsi daya, wanda aka sanar a ranar 24 ga watan Satumba da ya gabata.
Bayan da majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar amincewa da auren jinsin a cikin watan Yunin shekara ta 2024.
Thailand Ita ce kasa ta farko a kudu maso gabashin Asiya, kuma ta uku a nahiyar, bayan Taiwan da Nepal, da suka amince da auren jinsi kana ta 40 a cikin sahun kasaShen da suka amince da yin auren jinsin a duniya.