1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar bai daya ta shawo kan matsaloli a Turai

Abdullahi Tanko Bala
September 19, 2022

Hukumar tarayyar Turai ta gabatar da shawarar dokar bai daya ta samar da abubuwan da ake bukata daga mambobin kasashe domin shawo kan matsalolin da ka iya taso wa kasashen

Brüssel | Margrethe Vestager | EU-Kommissionsvizepräsidentin
Hoto: Dursun Aydemir/AA/picture alliance

A karkashin sabuwar dokar, ana iya tilasta wa kamfanonin Turai su bada fifiko wajen samar da muhimman kayayyakin da ake bukata da kuma tara su ko kuma su fuskanci tara.

Mataimakiyar shugabar hukumar tarayyar Turan Margrethe Vestager ta ce suna bukatar samar da yanayi da zai basu damar mayar da martani da daukar matakin bai daya cikin gaggawa.

Shawarar dokar gaggawa a kasashen masu amfani da kudin bai daya zai baiwa hukumar damar umartar kasashe su sauya fasalin kayayyakin da suke samarwa domin bada fifiko ga kayayyakin da ake fuskantar matsalar samuwarsu a kasuwanni.