An kafa dokar hana fita a Sri Lanka
September 22, 2024Gwamnatin kasar Sri Lanka ta kakaba dokar hana fitar dare a wannan Asabar duk da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasa cikin tsanaki da kwanciyar hankali. Gabanin rufe runfunan zaben an samu fitowar kimanin kaso 70 cikin 100 na masu kada kuri'a. Shugaba Ranil Wickremesinghe da yake rike da madafun ikon kasar yana neman wa'adi domin tabbatar da daidaita tattalin arzikin kasar.
Wickremesinghe mai shekaru 75 da haihuwa lokacin da ya karbi ragamar mulkin kasar tattalin atzikinta ya durkushe, abin da ya haifar boren da ya tilasta wa tsohon shugaban kasar Gotabaya Rajapaksa ajiye madafun iko a shekara ta 2022.
Hukumar zaben kasar ta Sri-Lanka ta ce za a iya samun sakamakon zaben a gobe Lahadi, zaben da mutane miliyan 17 suka cancanci kada kuri'a.