1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

An hana lullubin rufe fuska a Kazakhstan

Suleiman Babayo AH
June 30, 2025

Gwamnatin kasar Kazakhstan ta saka dokar hana mata saka lallubin da yake rufe fuska da ke nuna cewa an haramta saka hijabi na mata Muslmai da ke rufe.

Shugaba Kassym-Jomart Tokayev na kasar Kazakhstan
Shugaba Kassym-Jomart Tokayev na kasar KazakhstanHoto: Kazakhstan's Presidential Press Office/picture alliance/AP

Shugaba Kassym-Jomart Tokayev na kasar Kazakhstan ya saka hannu kan ayar dokar da ta hana rufe fuska a kasar, musamman batun lullubin mata na hijabi da yake rufe fuska, a duk bainar jama'a. Da wannan ayar doka mata Musulmai ba su da izinin rufe fuska da sunan hijabi, bisa kiyasi kasar tana da mabiya addinin Islama kimanin kaso 70 cikin 100 na 'yan kasar.

Karin Bayani: Kazakhstan za ta rubanya sayar wa Jamus mai

Haka ya saka kasar ta Kazakhstan ya bi sahun sauran kasashen yankin tsakiyar Asiya wajen hana mata rufe fuska da sunan addinin Islama, a kasashen da suke na galibi Musulmai.

Tun farko Shugaba Shugaba Kassym-Jomart Tokayev na kasar ta Kazakhstan ya dauki matakai da dama domin farfado da al'adun mutanen kasar, wadda take cikin kasashen Rushes-shiyar Tarayyar Soviet.