1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Cece-kuce kan dokar haraji

Uwais Abubakar Idris LM
November 30, 2024

Wata sabuwar takaddama ta kunno kai dangane da sabon kudirin dokar haraji da majalisar dattawan Najeriya ta amince ya kai mataki na gaba, inda yankin arewacin kasar ke adawa da shi.

Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Barin kudurorin guda hudu na dokar haraji ya tsallake matakin farko a majalisar dattawan Najeriya ya kara tayar da kurar adawar da ake yi da ita ta kara turnikewa. Tun bayan zaman da suka yi na daukar wannan mataki na barin kudurin ya kai karatu na biyu, kusan babu zancen da yafi daukar hankali da ya wuce wannan a yanzu. Kudurori guda hudu ne a cikin dokar, amma wanda yafi daukar hankali shi ne batun rabon harajin kayayyaki da gwamnatin ke son a sauya shi. 'Yan majalisar dattawan Najeriya daga yankin arewacin kasar na cikin matsin lamba da ma tsaka mai wuya a kan wannan batu, kokari na ganin ba su batawa gwamnati rai ba da kuma matakin da gwamnonin da sarakunan yankin suka dauka na lallai kar su bari a yi wa Arewa sakiyar da ba ruwa. Sun dakatar da taron manema labarai da kungiyar sanatoci daga arewacin kasar da ke da rinjaye a majalisar ta kira bagatatan, tare da bayar da uzurin suna tuntubar juna. A majalisar wakilan Najeriya dai ana can ana tafka muhawara a kan kuduri da ta sanya dakatar da shi a yanzu, inda majalisar wakilan za ta yi zama na musamman a makon gobe domin tafka muhawara. Abin jira a gani shi ne ko yawan 'yan majalisa daga Arewa zai iya yin tasiri, har ma su iya cirewa yankin kitse a wuta ko kuma su kasance taron yuyu ne.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani