Dokar Harbin 'yan tarzoma a Kenya
January 30, 2008Talla
Ƙasar Kenya dai na cigaba da fuskantar tashe tashen hankula a,wanda ya jagoranci umurnin gwamnati wa jamian 'yansanda na harbe duk masu tarzoma,yini guda bayan da tsohon sakatare General na Majalisar Ɗunkin Duniya Kofi Annan ya kaddamar da tattaunawar sulhu tsakanin ɓangarori biyu dake adawa. Wannan umurni na buɗa wuta akan masu tarzoma dake zama na biyun irin sa da gwamnatin Kenya ta kaddamar da ɓarkewar ricin sakamakon zaɓen na watan Disamba,yazo ne yini guda da kaddamar da tattaunawar sulhu tsakanin Mwai Kibaki da shugaban adawa Raila Odinga ,a karkashin jagorancin Kofi Annan. Bugu da kari umurnin yazo ne adaidai lokacin da a ƙasashen duniya da ƙungiyoyin kare hakkin jama'a ke cigaba dayin Allah wadan wannan rikici daya haddasa asaran rayukan mutane sama 1,00,baya ga wasu kusan dubu 250 da suka rasa matsugunnensu. Commandan rundunar 'yansan Kenya yace,waɗanda zasu faɗa cikin ayarin wannan umurnin na bindigewa sun haɗar da masu sace-sacen kayan jama'a,da masu kone konen gidaje da waɗanda ke ɗauke da makamai kana da kuma masu tare hanyoyi. To sai dai Hassan Omar Hassan dake hukumar kare hakkin jama'a ta Kenyan yace hakan ya saɓawa dokar kasa. "Duk wani umurni da zaa iya bayarwa ,dole ya kasance cikin tsarin dokar kasarmu,kuma dole ya kasance cikin kundun tsarin mulkin Kenya,domin amfani da bakin bindiga bazai shawo kan wannan rikici ba balle tabbatarwa da al'ummar Kenya tsaro". Tun daga jiya nedai jirage ƙirar saukar ungulu na dakarun soji sukayi ta buɗe wuta daga sararin samaniya ,a matsayin gargaɗi wa faɗan kabilanci dake gudana a garin Naivasha dake gabar teku. Rahotannin 'yansanda dai na nuni dacewar kimanin karin mutane 22 ne suka rasa rayukan su ,musamman ma a yankunan da 'yan adawan suke da mafi yawan magoya baya. To sai dai wa fitacciyar 'yar kare hakkin jama'a kuma wadda ta taba samun lambar yabo a fafutukar ta na neman zaman lafiya a Kenya,Mathai Wangari lokaci ne da Sojin ƙasar zasu taimakawa 'yansan. "Ina ganin lokacin jinkirtawa ya wuce,domin akwai zarge-zargen da akewa 'yansanda dangane da nuna wariya ayayin shawo kan wannan rikici,don haka nake ganin ya dace Hafsan sojin kasar yayi tunani dangane da shigar da jami'an soji a wajen shawo kan wannan rikici" Shugaban Adawa Raila Odinga ya bayyana cewar babu ɓacin rai ta kowace hanya dazai jagoranci kisan gilla,balle bada da damar zartar da hukuncin daukar fansa daga bangaren jama'a. Mai shiga tsakani kuma tsohon Sakatare General na Majalisar Ɗunkin Duniya Kofi Annan yayi imanin shawo kan wannan rikici cikin lokaci kaɗan. "Munyi imanin cewar za a warware wannan rikici bisa sadaukar da kai cikin shekara guda,amma muna fatan shawo kan matsalar siyasa cikin makonni huɗu masu gabatowa ko kuma kasa da Hakan"
Talla