An kafa dokar hana hawa babura a Zamafara
August 28, 2021Talla
Gwamnatin jihar Zamfara dake Arewa maso yammacin Najeriya ta sanya wasu dokoki a jihar da nufin magance matsalar tsaro da ta yiwa jhar dabaibayi. Matakin da ake ganin zai kasance mai tsauri na da niyar ne takaita yawaitar hare-haren da barayin daji da 'yan bindiga ke kaiwa fararen hulla tare da satar dukiyoyinsu a yankin.
A cikin wata hira da sashen hausa na DW, gwamnan Jihar Dr Bello Muhammad Matawalle, ya bayyana jerin wuraren da dokar ta shafa da suka hada da kasuwanni da hawan babura da kasuwancin shanu da na itace da sauransu. Masana tsaro dai na ganin idan Al'umma sukai hakuri suka bi Dokokin to za'a samu saukin matsalar duba da yadda matsalar tsaron jihar ke neman ta gagari kundila.