1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dokar zaben 2027 na fama da kwan-gaba kwan-baya

Uwais Abubakar Idris Mouhamadou Awal
February 18, 2026

Majalisar datawa ta yi gyara fuska ga dokar zabe don kauce wa gudanar da babban zaben 2027 a cikin azumin Ramadana, inda ta rage kwanakin da ya kamata INEC ta sanar da lokacin yin zabe daga kwanaki 350 zuwa 300.

'Yan Najeriya da dama sun yi korafi game da jadawalin zabe da INEC ta fara fitarwa
'Yan Najeriya da dama sun yi korafi game da jadawalin zabe da INEC ta fara fitarwaHoto: Christopher Onah/Focal Point Agency/IMAGO

Majalisar datawan Najriya ta dauki matakin gyaran fuska ga dokar zaben 2027 bayan korafe-korafe daga jam'iyyun adawa, malaman addini da sauran 'yan kasar a kan ranakun gudanar da zabubbukan da hukumar zabe mai zaman kanta ta sanar, wadanda suka fado a cikin azimin watan Ramadana.

Karin bayani: Najeriya: Ko INEC za ta gudanar da sahihin zabe a 2027?

Datawan sun yi gyaran fuska a kan sashe na 28 na dokar zaben Najeriya, wanda bisa haka aka rage kwanakin da doka ta tanadar na sanar da ranakun zaben daga kwanaki 350 zuwa 300. Sanata Yemi Adaramodu, kakakin majalisar datawan Najeriya ya ce: " Dalilin da ya sa muka mayar da shi kwanaki 300 saboda 'yan Najeriya ne, domin muna dokoki ne domin jama'a ba aljannu ba, tunda akwai wadanda suka ce in an yi zabe a wannan lokaci zai shafe su, ya zama dole muka canza domin ‘yan Najeriya''.

Matsin lamba ko kyautatawa a harkar zabe?

Majalisar dattawa ta sake wa sashe na 28 na dokar zabe fasali domin ya dace da bukatun 'yan adawaHoto: Wang Guansen/Xinhua/picture alliance

Matsin lamba da dagewar masu adawa na kin gudanar da zaben a lokacin azumin watan Ramadan a Najeriya sun kama hanyar samun biyan bukata, Bisa ga gyaran da aka yi a yanzu, majalisar datawa ta ba da dama ga hukumar zaben Najeriya ta INEC da ta sauya ranakun zaben da ta sanar a baya wanda ya tayar da kura.

Karin bayani: Takaddama kan ranakkun zaben 2027 a Najeriya

Dr Yunusa Tanko, jigo a jamiyyar adawa ta ADC ya ce: "Idan ka lura duk al'ummar Najeriya Kiristoci da Musulmi suna cikin azumi, suna cikin gajiya. Wannan zai rage musu karfin yadda za su fito su yi zabe da ba da goyon baya... Dole ne a yi la'akri da wannan."

A lokutan baya, Najeriya ta taba shirya zabe a lokacin azumin watan Ramadana. Amma masu adawa da hakan a yanzu na nuna tsoron iya fusknatar komabaya a bangaren masu zaben da tuni suka fara nuna gajiya da lamarin, baya ga yawan masu zuwa Umrah a kasar Saudiyya lokacin zaben.

INEC za ta kwaskware jadawalin zaben 2027

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta bayyana cewa tana duba wannan batu da a yanzu ta samu Karin karfi daga abin da majalisar datawan ta yi.

Karin bayani: Shin jadawalin zaben Najeriya na shekara ta 2027 zai yi aiki?

Hukumar zabe INEC na da aiki a gabanta wajen rejista da raba katunan kada kuri'aHoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP

A majalisar wakilai kuwa, ‘yan majalisa na jam'iyyar adawa sun yi tir da matakin da takwarorinsu na dattawa suka dauka inda suka yi amai suka lashe a game da batun aikewa da sakamakon zabe ta yanar gizo, inda 'yan majalisar wakilan suka bi abin da ta dattawa ta yi, ciki har da Hon Abdussamad Dasuki.

Dokar zaben Najeriya ta zama tamkar tsohuwar jakar da aka mika wa gyartai, wacce ke shan gyare-gyare a kasar a kokari na kyautata zabe da ‘yan adawa ke koken akwai kuduri na son rai da biyan bukatun wasu a kasar.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani