Tsara harkokin addinai a Jamhuriyar Nijar
October 25, 2019Duk da cewa akwai zaman lafiya tsakanin addinai a Jamhuriyar Nijar, amma kuma babbar matsalar ita ce ta rashin dokokin shari'a da ke ba da damar shirya mutane yadda kowa zai yi addininsa ba tare da tsangwame ba. Gwamnatin ta farka daga barci sakamakon ganin irin matsaloli da ake fuskanta a wasu kasashe makwabta, inda wasu ke fakewa da addini domin yin abin da bai dace ba.
Kiristoci da Musulmai dai a Jamhuriyar Nijar na tare da juna tun lokacin da kasar ta samu mulkin kai, inda suke zaune ba tare da wasu matsaloli ba. Batun hulda tsakanin addinai batu ne da ke da saukin gaske, duk wani abin da ya taso ta bangaren addini, za ka samu akwai masu tsawatawa.
A wannan zaman taro wanda ministan cikin gida Bazoum Mohamed ya jagoranta an samu halartar jakadun kasashen waje, sarakunan gargajiya da sauran masu fada a ji a fanni addinai.