1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Berlin na shirye-shiryen fuskantar shugabancin Trump kila

Hasselbach Christoph ZMA
July 19, 2024

Galibin ‘yan siyasar Jamus na fatan ganin an sake zaben shugaban Amurka Joe Biden na jam'iyyar Democrat. Amma kuma suna son su kasance cikin shirin ko ta kwana idan Donald Trump ya lashe zaben na watan Nuwanba.

Hoto: SvenSimon/picture alliance

 Akwai damuwa tsakanin mahukuntan na Berlin. Galibin 'yan siyasa na fatan Joe Biden na Democrat ya samu zarcewa a matsayin shugaban Amurka, wanda suka fi kusanci da siyasa. Sai dai a baya bayan-nan akwai abubuwa masu yawa da ke dasa ayar tambaya kan tabbatuwar hakan a zahiri, ciki har da yanayinsa da kalamansa wadanda ke cike tuntuben harshe. Kuma tun bayan yunkurin kisan gillar da aka yi wa Donald Trump, ko shakka babu ya kara masa farin jini da karin goyon baya bangaren Amurkawan. Babban taron jam'iyyar a Milwaukee a hukumance ya zabi  Trumpa matsayin dan takarar shugaban kasa na a zaben da ke tafe a watan Nuwamba.

Hoto: Evan Vucci/AP Photos/picture alliance

A fili ne dai a taron G7 da aka yi a Italiya a watan Yuni, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ayyana cewar zai fi son wa'adi na biyu ga Joe Biden. Wannan kuskure ne inji Jens Spahn daga babbar jam'iyyar adawa ta CDU wadda ita ce jam'iyyar da ke mulki a Berlin a lokacin mulkin Trump daga 2016 zuwa 2020. Spahn ya je birnin Milwaukee inda ya halarci babban taron jam'iyyar Republican saboda yana ganin   ya kamata siyasar Jamus ta sauya game da mu'amala da Trump. Ya ce "Zan iya cewa akwai yiwuwar ya zama shugaban Amurka na gaba, kuma bai kamata mu sake yin irin wannan kuskuren ba. A lokacin da ya zama shugaban kasa, babu wanda ya nemi wata hanyar alaka da tawagarsa. Babu wanda ya san abin da ke faruwa, kuma a wannan karon ya kamata mu sani tun da wuri kuma mu yi kokari wajen tuntubar shi da tawagarsa tun da wuri, kuma shi ya sa yana da muhimmanci mu kasance a nan."

Hoto: Gaelen Morse/REUTERS

Ba wai sake zaben Trump ne ya zame abun damuwa a Jamus kadai ba, har ma da nadin abokin takararsa J.D. Vance. Akwai fargaba game da batun tallafa wa Ukraine, alal misali. A taron tsaro na birnin Munich na nan Jamus a watan Fabrairu, Vance ya bayyana karara yadda shi da Trump za su yi saurin mika Ukraine wa Putin", kamar yadda shugaban jam'iyyar Green Ricarda Lang ya wallafa a shafin X. Tun a shekarar 2022 ne dai Vance cikin wani Podcast ya ce bai damu da abin da zai faru da Ukraine ba. "Amurka za ta sanya wasu muhimman abubuwa a nan gaba, Turai za ta kula da tsaron kanta sannan kuma ta dauki babban nauyin tallafa wa Ukraine. Dan siyasar jam'iyyar CDU Jens Spahn ya ce Trump tamkar kira ne ga Turai ta farka.

Hoto: Alexander Welscher/dpa/picture alliance

Ya ce "Amurka ita ce abokiyarmu mafi muhimmanci, don sune ke ba da tabbacin tsaro a Turai, gaskiyar magana ita ce, idan ba Amurka ba, Turai ba za ta iya samun tsaro ba. Don haka muna bukatar Amurka a matsayin abokiyar zamanmu, ko wane ne shugaban kasa."To sai dai har yanzu jami'an gwamnatin Jamus suna fatan cewa dan jam'iyyar Democrat Joe Biden, kamar yadda al'amura ke tafiya shi ne zai lashe zaben. Amma shakku na karuwa idan aka yi la'akari da raunin Biden, kuma 'yan Berlin din sun fara shirin ko ta kwana game da wannan sabon  yanayin da ke tafe.