1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Donald Trump na shirin zama shugaban Amirka na 47

Zainab Mohammed Abubakar
January 20, 2025

An kammala shirin rantsar da Donald Trump, wanda ya tsallake rijiya da baya a kan tuhumar da ake masa na aikata laifuka, a matsayin shugaban Amirka na shekaru hudu da ke tafe.

Hoto: Mark Wilson/Getty Images

Zababben shugaba Donald Trump karkashin tsarin jam'iyyarsa ta Republican na da niyyan sake fasalin tsarin lamuran kasar da ma dangantakarta da wasu kasashe.

Ana sa ran Trump zai dauki matakin gaggawa bayan bikin rantsuwar, na rattaba hannu kan wasu batutuwa da aka riga aka tsara da suka hadar da korara baki marasa takardu zaman Amurka, da rage kariyar ma'aikatan gwamnati, bisa alkawarin cewa wa'adinsa zai kawo  sabon yaanayi a tsarin rayuwar Amurka da wadata da mutunci daura da alfahari.

Yanayi na tsananin sanyi ya sa an mayar da bikin rantsar daTrump a cikin harabar majalisar kasar a karo na farkon faruwar irinsa a cikin shekaru 40, an maye gurbin faretin bukin da wani taron da za a yi a filin wasa na cikin gari.