Donald Trump ne dan takarar jam'iyyar Republican
July 22, 2016Talla
Da yake yin jawabi a gaban wakilan jam'iyyar kusan dubu biyu da kuma wasu miliyoyin Amirkawan a Cleveland da ke cikin Jihar Ohio,Trump ya ce aiki na farko da gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kai idna ya zama shugaban kasa, shi ne na kuubtar da al'ummar Amirka daga halin rashin tsaro na kisan ba gayra na jama'a da kuma ta'addanci da ke zama babbar barazana ga rayuwar jama'a.