1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Amurka: Kotu za ta fara sauraron Donald Trump

Abdourahamane Hassane
April 22, 2024

A ranar Litinin(22.04.2024) ne ake fara shari'ar mai cike da tarihi ta tsohon shugaban Amurka Donald Trump a birnin New York kan zargin da ake yi masa.

USA | Schweigegeldprozesses gegen den ehemaligen US-Präsidenten Trump
Hoto: EPA/SARAH YENESEL

Ana zargin tsohon shugaban na  Amurka da  biyan kudade  dala  dubu130,000 ga wata tsohuwar tauraron wasannin batsa  wato Stormy Daniels kafin zaben shekara ta 2016 a madadin ta yi shiru game da wata alaka da suka yi, ta lalata shekaru goma da suka gabata.Bayan mako na farko da aka keɓe don zaɓen alkalai, an saita matakin: alkalai 12, maza bakwai da mata biyar da za su su yanke hukunci a kan ɗan takarar jam'iyyar  Republican a zaben shugaban ƙasa.  Masu aiko da rahotanin sun ce shari'ar tana yin barazana ga Donald Trump na fuskantar hukuncin ɗauri a gidan kurkuku, 'yan watanni kafin zaben shugaban kasar da za a yi a cikin watan   Nuwamba da ke tafe.