Donald Tusk zai ci gaba da jagoranci a EU
March 9, 2017Talla
A yayin wani taron koli da ya gudana a wannan Alhamis a birnin Brussels na kasar Beljiyam, shugabannin kasashen Turai 27 ne suka zabi Tusk dan asalin kasar Poland domin ya sake jagorantar hukumar hadin kan Turai na tsawon shekaru biyu da rabi.
To sai dai wannan zabe na Tusk, na ci gaba da shan suka daga wakilan kasarsa ta haihuwa wato Poland. Amma shugaban ya wallafa a shafinsa na twitter jim kadan bayan zabensa cewar zai iya bakin kokarinsa na ganin ya inganta Tarayyar kasahen Turai.