Doumbouya da ya yi juyin mulki a Guinea ya lashe zabe
December 31, 2025
Hukumar zaben kasar ta bayyana Doumbouya a matsayin wanda ya samu nasara da kashi 86.71 bisa 100 na yawan kuri'un da aka kada. Doumbouya wanda ya kwace ragamar shugabancin kasar ta hanyar juyin mulki a 2021, bayan hambarar da gwamnatin Alpha Conde, ya rikide zuwa farar hula domin ci gaba da jan ragamar kasar a wani salo na dimukuradiyya mai kama da kama karya. Dama dai an yi hasashen cewa shi ne zai lashe zaben ba tare da hamayya ba.
Karin bayani:Al'ummar Guinea sun fara kada kuri'ar zaben shugaban kasa
Gabanin gudanar da zaben shugaban kasar na Guinea, an haramta wa ‘yan adawa da dama tsayawa takara, a yayin da wasu suka tsere zuwa kasashen ketare domin neman mafakar siyasa. Sannan gamayyar shugabannin jam'iyyun adawa sun bukaci daukacin al'umma da su kauracewa zaben.
Tsohon minista a gwamnatin Guinea, Yero Balde, Shi ne ya zo na biyu a zaben, inda ya samu kashi 6.51 bisa 100 na yawan kuri'un da aka kada.
.