1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Mahama na kan gaba a zaben Ghana

Suleiman Babayo AH
December 9, 2024

Tsohon shugaban Ghana Dramani Mahama ya lashe zabe yayin da ake jiran cikekken sakamakon zaben.

Ghana  | Magoya bayan John Mahama
Magoya bayan John Mahama a zaben kasar GhanaHoto: OLYMPIA DE MAISMONT/AFP

A kasar Ghana ana jiran cikekken sakamakon zaben kasar da ta tabbata cewa tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama mai shekaru 66 da haihuwa, ya sake kadowa kan madafun iko, wanda ya yi alkawarin farfado da tattalin arzikin kasar da ke yankin yammacin Afirka.

Karin Bayani: Mataimakin shugaban Ghana ya rungumi kaddara

Jam'iyyar NDC mai adawa ta Dramani Mahama take kan gaba a kujerun majalisar dokokin, yayin da jam'iyya mai mulki na NPP take matsayi na biyu, kuma tun farko dan takarar jam'iyya mai mulki Mahamudu Bawumia mataimakin shugaban kasa ya amince da shan kaye gabanin tattara sakamakon zaben a hukumance. Shi dai Shugaba Nana Akufo-Addo baya cikin 'yan takara saboda yana kammala wa'adinsa na biyu kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.