1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

DRC: An bukaci a yanke wa Kabila hukuncin kisa

August 23, 2025

Ana zargin tsohon shugaban na Kwango Joseph Kabila da aikata laifukan yaki da cin amanar kasa da kuma yunkurin tayar da fitina a gabashin kasar.

Kongo Goma 2025 | Treffen von Joseph Kabila mit Religionsführern
Hoto: Jospin Mwisha/AFP

Hukumomi a Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango sun bakaci kotun kolin soji ta yanke wa tsohon shugaban kasar Joseph Kabila hukuncin kisa, kan zargin hada baki da 'yan tawayen M23 masu samun goyon bayan Rwanda da ke tayar da kayar baya a gabashin kasar.

A jiya Juma'a a ce dai mai shigar da kara da ke wakiltar gwamnatin Kwango Janar Lucien Rene Likulia, ya bukaci alkalan kotun kolin sojin kasar da su yanke wa Kabila wannan hukunci saboda abin da ya kira ''aikata laifukan yaki da cin amanar kasa da kuma yunkurin tayar da fitina''.

A karshen watan Mayu da ya gabata ne dai Joseph Kabila da ya shafe shekaru fiye da biyu yana zaune a kasashen ketare ya bayyana a birnin Goma na gabashin Kwango wanda ke karkashin ikon 'yan tawayen M23, wadanda hare-harensu suka yi ajalin dubban mutane tare da raba miliyoyi da matsugunensu.

Karin bayani: Kwango: Kabila a birnin Goma 

Tun a ranar 25 ga watan Yuli ne dai aka bude shari'ar Joseph Kabila mai shekaru 53 a duniya ba tare da halartarsa ba, sai dai magoya bayansa sun ce ana kokarin yi masa bita da kulli ne kawai saboda dalilai na siyasa.

Karin bayani:  Kwango: An dakatar da jam'iyyar PPRD ta Kabila